Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 5:14-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

15. Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa yake yi, har taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa domin su saurare shi, a kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu.

16. Amma shi, sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu'a.

17. Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan.

18. Sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan shimfiɗa, suna ƙoƙari su shigar da shi su ajiye shi a gaban Yesu.

19. Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu.

20. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.”

21. Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?”

22. Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?

23. Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?

24. Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.”

25. Nan take ya tashi a gaban idonsu, ya ɗauki abin kwanciyarsa, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah.

26. Sai suka yi mamaki matuƙa, su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya kama su, suka ce, “Yau mun ga al'ajabai!”

27. Bayan haka ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.”

Karanta cikakken babi Luk 5