Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 3:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”

10. Sai taron suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi ke nan?”

11. Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.”

12. Masu karɓar haraji ma suka zo a yi musu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?”

13. Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.”

14. Waɗansu soja ma suka tambaye shi, “To, mu fa, me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku yi wa kowa ƙwace ko ƙazafi. Ku dai dangana da albashinku.”

15. Da yake mutane duk sun zaƙu, kowa yana wuswasi a ransa a game da Yahaya, ko watakila shi ne Almasihu,

Karanta cikakken babi Luk 3