Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 21:22-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.

23. Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama'an nan.

24. Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”

25. “Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al'ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa.

26. Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al'amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.

27. A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.

28. Sa'ad da waɗannan al'amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”

29. Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa,

30. da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan.

31. Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan al'amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato.

Karanta cikakken babi Luk 21