Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 18:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Amma Yesu ya kira 'yan yara wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.

17. Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

18. Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”

19. Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci, sai Allah kaɗai.

20. Kā dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi zina. Kada ka yi kisankai. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

21. Sai ya ce, “Ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.”

22. Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”

23. Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske.

24. Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!

25. Ai, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

26. Waɗanda suka ji wannan magana suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

27. Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”

28. Sai Bitrus ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka.”

Karanta cikakken babi Luk 18