Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 16:6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya ce, ‘Garwa ɗari ta mai.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubutu hamsin,’

7. Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ake binka?’ Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’

8. Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.

9. Ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, ko da yake aba ce wadda take iya aikata mugunta, don sa'ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.

10. “Wanda yake da aminci a ƙaramin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, marar gaskiya ne a babban abu.

11. Idan fa ba ku yi aminci da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?

12. In kuma ba ku yi aminci da kayan wani ba, wa zai ba ku halaliyarku?

13. Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

14. Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.

15. Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.

16. “Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki.

17. Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”

18. “Kowa ya saki mata tasa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.”

19. “An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana.

20. An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li'azaru, wanda duk jikinsa miki ne.

21. Shi kuwa yana marmarin ya ƙoshi da suɗin mai arzikin nan. Har ma karnuka sukan zo suna lasar miyakunsa.

Karanta cikakken babi Luk 16