Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 16:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

14. Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.

15. Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.

16. “Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki.

17. Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”

18. “Kowa ya saki mata tasa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.”

19. “An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana.

20. An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li'azaru, wanda duk jikinsa miki ne.

21. Shi kuwa yana marmarin ya ƙoshi da suɗin mai arzikin nan. Har ma karnuka sukan zo suna lasar miyakunsa.

22. Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala'iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin Ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.

23. Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a wurinsa.

24. Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko Li'azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’

25. Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.

Karanta cikakken babi Luk 16