Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 1:5-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.

6. Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.

7. Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.

8. Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidima tasa ta firist, a sa'ad da hidimar ta kewayo kan ƙungiyarsu,

9. bisa ga al'adar hidimar firistoci, sai kuri'a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare.

10. A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama'a suna waje, suna addu'a,

11. sai wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare.

12. Da Zakariya ya gan shi ya firgita, tsoro ya kama shi.

13. Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.

14. Za ka yi murna da farin ciki,Mutane da yawa kuma za su yi farin ciki da haihuwa tasa.

15. Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji,Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba.Za a cika shi da Ruhu Mai TsarkiTun yana cikin uwa tasa.

16. Zai kuma juyo da Isra'ilawa da yawa ga Ubangiji Allahnsu.

17. Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya.Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu,Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai,Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”

18. Sai Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kwana biyu.”

19. Sai mala'ikan ya amsa ya ce, “Ni ne Jibra'ilu da yake tsaye a gaban Allah. An aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir.

20. To, ga shi, za ka bebance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al'amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.”

21. Jama'a suna ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Haikali.

22. Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana.

Karanta cikakken babi Luk 1