Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 1:12-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. kuna gode wa Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gādon tsarkakan da suke a cikin haske.

13. Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,

14. wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato, gafarar zunubanmu.

15. Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba,

16. don ta gare shi ne aka halicci dukkan kome, abubuwan da suke a sama da abubuwan da suke a ƙasa, masu ganuwa da marasa ganuwa, ko kursiyai, ko masu mulki, ko masarauta, ko masu iko, wato, dukkan abubuwa an halicce su ne ta wurinsa, shi ne kuma makomarsu.

17. Shi ne a gaba da dukkan abubuwa, dukkan abubuwa kuma shi ne yake riƙe da su.

18. Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici.

19. A gare shi dukkan cikar Allah ta tabbata, domin Allah yana farin ciki da haka,

20. da nufin ta wurinsa, Allah yă sulhunta dukkan abubuwa da shi kansa, na ƙasa ko na sama, yana ƙulla zumunci ta wurin jininsa na gicciye.

21. Ku kuma dā a rabe kuke da Allah, maƙiyansa a zuci, masu mugun aiki.

22. Amma a yanzu ya sulhunta ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato, ta wurin mutuwarsa, domin ya miƙa ku tsarkakakku, marasa aibu, marasa abin zargi kuma a gabansa.

23. Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.

24. To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,

25. wadda na zama mai hidimarta bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da Maganar Allah sosai,

26. wato, asirin nan da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, amma a yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa.

27. Su ne Allah ya so ya sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al'ummai, asirin nan kuwa shi ne Almasihu a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.

28. Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu.

29. Saboda wannan nake shan wahala, nake fama da matuƙar himma, wadda yake sa mini ta ƙarfin ikonsa.

Karanta cikakken babi Kol 1