Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 3:2-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu saboda bin Shari'a ne, ko kuwa saboda gaskatawa ga maganar da kuka ji?

3. Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa?

4. Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banzan ne!

5. Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?

6. Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”

7. Wato kun ga ashe, masu bangaskiya su ne 'ya'yan Ibrahim.

8. A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al'ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al'ummai albarka.”

9. To, ashe, masu bangaskiya su ne aka yi wa albarka a game da Ibrahim mai bangaskiyar nan.

10. Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.”

11. To, a fili yake, ba mai samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, domin “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”

12. Shari'a kuwa ba ta dangana ga bangaskiya ba, domin ta ce, “Wanda ya aikata ta, ta gare ta ne zai rayu.”

13. Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”

14. An yi wannan kuwa domin albarkar nan da aka yi wa Ibrahim ta saukar wa al'ummai ta wurin Almasihu Yesu, mu kuma ta hanyar bangaskiya mu sami Ruhun nan da aka yi alkawari.

15. To, 'yan'uwa, bari in yi muku misali. Ko alkawari na mutum ne kawai, in dai an riga an tabbatar da shi, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai.

16. To, alkawaran nan, an yi wa Ibrahim ne, da kuma wani a zuriyarsa. Ba a ce, “Da zuriya” ba, kamar suna da yawa. A'a, sai dai ɗaya kawai, aka ce, “Wani a zuriyarka,” wato Almasihu.

17. Ga abin da nake nufi. Shari'ar nan, wadda ta zo shekara arbaminya da talatin daga baya, ba ta shafe alkawarin nan da Allah ya tabbatar tun tuni ba, har da za ta wofinta shi.

18. Don da gādon nan ta hanyar Shari'a yake samuwa, ashe, da ba zai zama na alkawarin ke nan ba. Amma Allah ya bai wa Ibrahim ta wurin alkawari ne.

Karanta cikakken babi Gal 3