Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 5:29-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.

30. Allahn kakanninmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin kafe shi a jikin gungume.

31. Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.

32. Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al'amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”

33. Da suka ji haka, sai suka husata ƙwarai da gaske, suna so su kashe su.

34. Amma wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama'a suke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna.

35. Sa'an nan ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku kula fa da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.

36. Shekarun baya wani mutum ya ɓullo, wai shi Tudas, yana mai da kansa wani abu, wajen mutum arbaminya kuma suka bi shi, amma aka kashe shi, mabiyansa kuwa aka watsa su, suka lalace.

37. Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su.

38. To, yanzu ma, ina gaya muku, ku fita sha'anin mutanen nan, ku ƙyale su. Idan dai niyyarsu ko aikinsu na mutum ne, ai, zai rushe,

39. amma in na Allah ne, ba dama ku rushe su. Kada fa a same ku kuna gāba da Allah.”

40. Sai suka bi shawara tasa, suka kuma kirawo manzannin, suka yi musu dūka, suka kwaɓe su kada su ƙara magana da sunan Yesu, sa'an nan suka sake su.

41. To, suka tashi daga gaban majalisar, suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulakanci saboda sunan Yesu.

42. Kowace rana kuwa, ko a Haikali ko a gida, ba su daina koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu ba.

Karanta cikakken babi A.m. 5