Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 5:10-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Nan tāke, ta fāɗi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo, suka iske ta matacciya, suka ɗauke ta suka fitar da ita, suka binne ta a jikin mijinta.

11. Sai matsanancin tsoro ya kama dukan Ikkilisiyar, da kuma dukan waɗanda suka ji labarin waɗannan abubuwa.

12. To, an yi mu'ujizai da abubuwan al'ajabi masu yawa a cikin mutane ta hannun manzanni. Dukansu kuwa da nufi ɗaya sukan taru a Shirayin Sulemanu.

13. Amma a cikin sauran mutane ba wanda ya yi ƙarfin halin shiga cikinsu, duk da haka kuwa jama'a suna girmama su.

14. Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa suke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama'a masu yawan gaske mata da maza.

15. Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya tafarku, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwa tasa ma ta bi ta kan waɗansunsu.

16. Mutane kuwa suka yi ta taruwa daga garuruwan da suke kewayen Urushalima, suna ta kawo marasa lafiya da waɗanda baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, dukansu kuwa aka warkar da su.

17. Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato 'yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya,

18. suka kama manzannin, suka sa su kurkuku.

19. Amma da daddare sai wani mala'ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce,

20. “Ku tafi, ku tsaya a cikin Haikali, ku sanar da jama'a duk maganar wannan rai.”

21. Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa.To, babban firist ya fito, shi da waɗanda suke tare da shi, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Isra'ilawa, suka aika kurkuku a kawo su.

22. Amma da dogaran Haikali suka je, ba su same su a kurkukun ba, suka dawo suka ba da labari, suka ce,

23. “Mun iske kurkukun a kulle sosai, masu tsaro kuma na tsaro a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.”

24. To, da shugaban dogaran Haikali da manyan firistocin suka ji haka, suka ruɗe ƙwarai a game da su, suka rasa inda abin zai kai.

Karanta cikakken babi A.m. 5