Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 26:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. “Saboda haka, ya sarki Agaribas, ban ƙi biyayya ga wahayin nan da ya zo mini daga Sama ba.

20. Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.

21. Saboda wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a Haikali, har suna neman kashe ni.

22. Da na sami taimakon Allah kuwa, ga ni a nan har yanzu, ina shaida wa babba da yaro, ba na faɗar kome sai abin da annabawa da Musa suka ce zai auku,

23. cewa dai lalle ne Almasihu yă sha wuya, shi ne kuma zai fara tashi daga matattu, ya sanar da jama'ar nan da al'ummai haske.”

24. Bulus na cikin kawo hanzarinsa, sai Festas ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Bulus, kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”

25. Amma Bulus ya ce, “Ya mafifici Festas, ai, ban ruɗe ba, gaskiya nake faɗa, cikin natsuwa kuwa.

26. Ai, al'amarin nan sananne ne ga sarki, ina kuma masa magana gabagaɗi ne, gama na tabbata ba abin da ya kuɓuce wa hankalinsa cikin al'amarin nan, don wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba.

27. Ya sarki Agaribas, ka gaskata annabawa? Na dai sani ka gaskata.”

Karanta cikakken babi A.m. 26