Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 20:1-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan hargowar nan ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.

2. Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa masu zuciya ƙwarai, ya zo ƙasar Hellas,

3. ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa'ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.

4. Subataras Babiriye, ɗan Burus, shi ya raka shi, tare da Aristarkus da Sakundas, mutanen Tasalonika, da Gayus Badarbe, da Timoti, har ma da Tikikus da Tarofimas, mutanen Asiya,

5. waɗanda suka riga tafiya suka jira mu a Taruwasa.

6. Mu kuwa muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa, bayan idin abinci marar yisti, muka iske su a Taruwasa bayan kwana biyar. Nan muka zauna har kwana bakwai.

7. A ranar farko ta mako kuma, da muka taru don gutsuttsura gurasa, Bulus ya yi masu jawabi, don ya yi niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta jan jawabin nasa har tsakar dare.

8. Akwai kuwa fitilu da yawa a benen da muka taru.

9. Da wani saurayi a zaune a kan taga, mai suna Aftikos, sai barci ya ci ƙarfinsa sa'ad da Bulus yake ta tsawaita jawabi, da barci mai nauyi ya kwashe shi, sai ya faɗo daga can hawa na uku, aka ɗauke shi matacce.

10. Amma Bulus ya sauka ƙasa, ya miƙe a kansa, ya rungume shi, ya ce, “Kada ku damu, ai, yana da rai.”

11. Da Bulus ya koma sama, ya gutsuttsura gurasa ya ci, ya daɗe yana magana da su, har gari ya waye, sa'an nan ya tashi.

12. Sai suka tafi da saurayin nan a raye, daɗin da suka ji kuwa ba kaɗan ba ne.

13. Mu kuwa muka yi gaba zuwa jirgin, muka miƙe sai Asus da nufin ɗaukar Bulus daga can, don dā ma haka ya shirya, shi kuwa ya yi niyyar bi ta ƙasa.

14. Da ya same mu a Asus, muka ɗauke shi a jirgin, muka zo Mitilini.

15. Daga nan kuma muna tafe a jirgin ruwan dai, kashegari kuma sai ga mu daura da tsibirin Kiyos. Kashegari kuma, ga mu a tsibirin Samas, kashegari kuma sai Militas.

16. Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Afisa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, in mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.

17. Daga Militas ne ya aika Afisa a kira masa dattawan Ikkilisiya.

Karanta cikakken babi A.m. 20