Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 19:27-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.”

28. Da suka ji haka suka hasala ƙwarai, suka kuma ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

29. Sai garin duk ya ruɗe, jama'a suka ruga zuwa dandali da nufi ɗaya, suna jan Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya, abokan tafiyar Bulus.

30. Bulus ya so shiga taron nan, amma masu bi suka hana shi.

31. Waɗansu zaɓaɓɓun mutanen ƙasar Asiya, waɗanda suke abokansa, su ma suka aika masa, suka roƙe shi kada ya kuskura ya shiga dandalin nan.

32. Taron kuwa, waɗansu suka ta da murya su ce kaza, waɗansu su ce kaza, don duk taron a ruɗe yake, yawancinsu ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba.

33. Da Yahudawa suka gabatar da Iskandari, waɗansu suka ɗauka a kan shi ne sanadin abin. Iskandari kuwa ya ɗaga hannu a yi shiru, don ya kawo musu hanzari,

34. amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa'a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

35. To, da magatakardan garin ya kwantar da hankalin jama'a, ya ce, “Ku mutanen Afisa! Wane mutum ne bai san cewa musamman birnin Afisawa ne suke kula da haikalin mai girma Artimas ba, da kuma dutsen nan da ya faɗo daga sama?

36. To, da yake ba dama a yi musun waɗannan abubuwa, ai, ya kamata ku natsu, kada ku yi kome da garaje.

37. Ga shi, kun kawo mutanen nan, su kuwa ba su yi sata a ɗakin uwargijiya ba, ba su kuma saɓi uwargijiyarmu ba.

38. To, in Dimitiriyas da abokan sana'arsa suna da wata magana a game da wani, ai, ga ɗakin shari'a a buɗe, ga kuma mahukunta, sai su kai ƙara.

Karanta cikakken babi A.m. 19