Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 17:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, da suka bi ta Amfibolis da Aboloniya, suka isa Tasalonika, inda wata majami'ar Yahudawa tāke.

2. Sai Bulus ya shiga wurinsu kamar yadda ya saba, Asabar uku a jere yana muhawwara da su daga cikin Littattafai,

3. yana yi musu bayani, yana kuma tabbatarwa, cewa lalle ne, Almasihu yă sha wuya, ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Yesun nan da nake sanar muku, shi ne Almasihu.”

4. Sai waɗansunsu suka amince, suka koma wajen Bulus da Sila, haka kuma babban taron Helenawa masu ibada, da manyan mata ba kaɗan ba.

5. Amma Yahudawa, saboda kishi, suka ɗibi waɗansu ashararai, 'yan iska, suka tara jama'a suka hargitsa garin kaf, suka fāɗa wa gidan Yason, suna nemansu don su fito da su gaban taron jama'a.

6. Da ba su same su ba, suka jawo Yason da waɗansu 'yan'uwa, har gaban mahukuntan garin, suna ihu suna cewa, “Mutanen nan masu ta da duniya a tsaye, ga su sun zo nan ma,

7. har ma Yason ya sauke su! Dukansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wani ne sarki, wai shi Yesu.”

8. Da mutanen gari da mahukunta suka ji wannan, hankalinsu ya tashi.

9. Ba su sake su ba, sai da suka karɓi kuɗin lamuni a hannun Yason da sauransu.

10. Nan da nan kuwa da dare ya yi, 'yan'uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Biriya. Da suka isa can kuma suka shiga majami'ar Yahudawa.

11. To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.

12. Saboda haka da yawa daga cikinsu suka ba da gaskiya, har da waɗansu Helenawa ba kaɗan ba, mata masu daraja, da kuma maza.

13. Amma da Yahudawan Tasalonika suka ji labari Bulus yana sanar da Maganar Allah a Biriya ma, suka je suka zuga taro masu yawa a can ma, suna ta da hankalinsu.

14. Nan da nan kuwa 'yan'uwa suka tura Bulus bakin bahar, amma Sila da Timoti suka dakata a nan.

15. Waɗanda suka rako Bulus kuwa, sai da suka kai shi har Atina. Bayan Bulus ya yi musu saƙon umarni zuwa wurin Sila da Timoti, cewa su zo wurinsa da gaggawa, suka tafi.

16. To, sa'ad da Bulus yake dākonsu a Atina, ya ji haushi ƙwarai da ya ga ko'ina gumaka ne a birnin.

Karanta cikakken babi A.m. 17