Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 12:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Da ya ƙwanƙwasa ƙofar zauren, wata baranya mai suna Roda ta zo ji ko wane ne.

14. Da ta shaida muryar Bitrus, ba ta buɗe ƙofar ba don murna, sai ta koma ciki a guje, ta ce Bitrus na tsaye a ƙofar zaure.

15. Sai suka ce mata, “Ke dai akwai ruɗaɗɗiya.” Ita kuwa ta nace a kan shi ne. Su kuwa suka ce, “To, mala'ikansa ne!”

16. Bitrus dai ya yi ƙwanƙwasawa, da suka buɗe suka gan shi, suka yi ta al'ajabi.

17. Shi kuwa ya ɗaga musu hannu su yi shiru, ya kuma bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakubu da 'yan'uwa waɗannan abubuwa.” Sa'an nan ya tashi ya tafi wani wuri.

18. Da gari ya waye kuwa ba ƙaramar rigima ce ta tashi tsakanin sojan nan ba, kan abin da ya sami Bitrus.

19. Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, ya yi ta tuhumar masu tsaron, ya kuma yi umarni a kashe su. Sa'an nan ya tashi daga ƙasar Yahudiya ya tafi Kaisariya, ya yi 'yan kwanaki a can.

20. To, Hirudus ya yi fushi ƙwarai da mutanen Taya da na Sidon. Suka zo wurinsa da nufi ɗaya. Bayan sun rinjayi Bilastasa, sarkin fāda, suka nemi zaman lafiya, domin ga ƙasar sarkin nan suka dogara saboda abincinsu.

Karanta cikakken babi A.m. 12