Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, ya yi ta tuhumar masu tsaron, ya kuma yi umarni a kashe su. Sa'an nan ya tashi daga ƙasar Yahudiya ya tafi Kaisariya, ya yi 'yan kwanaki a can.