Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 2:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. In ba mu da aminci, shi kam ya tabbata mai aminci,Domin ba zai yi musun kansa ba.”

14. Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.

15. Ka himmantu, ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma'aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara Maganar gaskiya daidai.

16. Ka yi nesa da masu maganganun banza na sāɓo. Sai daɗa jan mutane zuwa ga rashin bin Allah suke yi,

17. maganarsu takan haɓaka kamar gyambo. A cikinsu har da Himinayas da Filitas,

18. waɗanda suka bauɗe wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da bangaskiyar waɗansu.

19. Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”

20. A babban gida, ba kayan zinariya da na azurfa ne kawai ba, har ma da na itace da na yumɓu, waɗansu don aikin ɗaukaka, waɗansu kuwa don ƙasƙantaccen aiki.

21. Kowa yă tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai zama ma'aikaci mai daraja, tsarkakakke, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.

22. Don haka, sai ka guje wa mugayen sha'awace-sha'awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.

Karanta cikakken babi 2 Tim 2