Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 6:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Kamar ma ba a san mu ba, an kuwa san mu sarai, kamar a bakin mutuwa muke, ga shi kuwa, muna a raye, ana ta horonmu, duk da haka ba a kashe mu ba,

10. kamar muna baƙin ciki, kullum kuwa farin ciki muke yi, kamar matalauta muke, duk da haka kuwa muna arzuta mutane da yawa, kamar ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

11. Ya ku Korantiyawa, ba mu ɓoye muku kome ba, mun saki zuciya da ku ƙwarai.

12. Ai, ba wata rashin yarda a zuciyarmu, sai dai a taku.

13. Ina roƙonku kamar 'ya'yana, ku ma ku saki zuciya da mu.

14. Kada ku yi cuɗanya marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

15. Ina kuma jiyayyar Almasihu da iblis? Me kuma ya haɗa mai ba da gaskiya da marar ba da gaskiya?

16. Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce,“Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu,Zan kuma kasance Allahnsu,Su kuma su kasance jama'ata.

17. Saboda haka, sai ku fito daga cikinsu,Ku keɓe, in ji Ubangiji,Kada ku ko taɓa wani abu marar tsarki,Ni kuwa in yi na'am da ku,

18. In kasance Uba a gare ku,Ku kuma ku kasance 'ya'yana, maza da mata,In ji Ubangiji Maɗaukaki.”

Karanta cikakken babi 2 Kor 6