Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 6:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matuƙar jurewa, da shan wahala, da ƙuntata, da masifu,

5. da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.

6. Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka, da sani, da haƙuri, da kirki, da Ruhu Mai Tsarki, da sahihiyar ƙauna,

7. da maganar gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu.

8. Ana ɗaukaka mu, ana kuma wulakanta mu, ana yabonmu, ana kuma kushenmu. An ɗauke mu kamar mayaudara, mu kuwa masu gaskiya ne.

9. Kamar ma ba a san mu ba, an kuwa san mu sarai, kamar a bakin mutuwa muke, ga shi kuwa, muna a raye, ana ta horonmu, duk da haka ba a kashe mu ba,

10. kamar muna baƙin ciki, kullum kuwa farin ciki muke yi, kamar matalauta muke, duk da haka kuwa muna arzuta mutane da yawa, kamar ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

11. Ya ku Korantiyawa, ba mu ɓoye muku kome ba, mun saki zuciya da ku ƙwarai.

12. Ai, ba wata rashin yarda a zuciyarmu, sai dai a taku.

13. Ina roƙonku kamar 'ya'yana, ku ma ku saki zuciya da mu.

14. Kada ku yi cuɗanya marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

15. Ina kuma jiyayyar Almasihu da iblis? Me kuma ya haɗa mai ba da gaskiya da marar ba da gaskiya?

Karanta cikakken babi 2 Kor 6