Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 3:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. domin shi ne ya iyar mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari, ba alkawarin rubutacciyar ka'ida ba, sai dai na Ruhu. Don kuwa rubutacciyar ka'ida, kisa take yi, Ruhu kuwa, rayarwa yake yi.

7. Aka zana hidimar Shari'ar Musa, wadda ƙarshenta mutuwa ce, a allunan duwatsu. An bayyana hidimar nan da babbar ɗaukaka, har Isra'ilawa suka kasa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta (ga ta kuwa mai shuɗewa ce).

8. Ina misalin fifikon hidimar Ruhu mafi ɗaukaka?

9. Gama idan hidimar da take jawo hukunci abar ɗaukakawa ce, to, lalle hidimar da take jawo samun adalcin Allah ta fi ta ɗaukaka nesa.

10. Hakika a wannan hali, abin da dā take da ɗaukaka ya rasa ɗaukaka sam, saboda mafificiyar ɗaukakar da ta jice ta.

11. Domin in aba mai shuɗewa an bayyana ta da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwamamme, lalle ne ya kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa.

12. Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai.

13. Ba kamar Musa muke ba, wanda ya rufe fuskarsa da mayafi, don kada Isr'ailawa su ga ƙarewar ɗaukakar nan mai shuɗewa.

Karanta cikakken babi 2 Kor 3