Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 1:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Don haka, lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da yake kun san su, kun kuma kahu a kan gaskiyar nan da kuke da ita.

13. A ganina daidai ne, muddin ina raye a cikin jikin nan, in riƙa faɗakar da ku ta hanyar tuni,

14. da yake na sani na yi kusan rabuwa da jikin nan nawa, kamar yadda Ubangijinmu Yesu Almasihu ya yi mini ishara.

15. Aniyata ce, a kowane lokaci ku iya tunawa da waɗannan abubuwa bayan ƙauracewata.

16. Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa'ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran.

17. Domin sa'ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,”

18. mu ne muka ji muryar nan da aka saukar daga sama, don muna tare da shi a kan tsattsarkan Dutsen nan.

19. Har wa yau kuma, aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku, ku mai da hankali a gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranar nan, gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku.

20. Da farko dai, lalle ne ku fahimci wannan cewa, ba wani annabci a Littattafai da za a iya fassarawa ta ra'ayin mutum.

21. Domin ba wani annabcin da ya taɓa samuwa ta nufin mutum, sai dai mutane ne Ruhu Mai Tsarki yake izawa, Allah yana magana ta bakinsu.

Karanta cikakken babi 2 Bit 1