Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 9:10-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ba saboda mu musamman yake magana ba? Hakika saboda mu ne aka rubuta. Ai, ya kamata mai noma yă yi noma da sa zuciya, mai sussuka kuma yă yi sussuka da sa zuciya ga samun rabo daga amfanin gonar.

11. Da yake mun shuka iri na ruhu a zuciyarku, to, wani ƙasaitaccen abu ne, in mun mori amfaninku irin na duniya?

12. Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba?Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa.

13. Ashe, ba ku sani ba, masu hidima a Haikali daga nan suke samun abincinsu? Masu hidimar bagadi kuma, a nan suke samun rabo daga hadayar da aka yanka?

14. Haka nan kuma Ubangiji ya yi umarni, cewa, ya kamata masu sanar da bishara, a cishe su albarkacin bishara.

15. Amma ni kam, ban mori ko ɗaya daga cikin halaliyan nan ba, ba kuma ina rubuta wannan ne, don a yi mini haka ba. Ai, gara in mutu a kan wani ya banzanta mini fahariyata.

16. Don ko da yake ina yin bishara, ba na fahariya da haka, gama tilas ne a gare ni. Kaitona in ba na yin bishara!

17. Da da ra'ina nake yi, da sai a biya ni. Amma da yake ba da ra'ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan.

18. Ina kuma hakkina? To, ga shi. A duk lokacin da nake yin bishara, sona in yi ta a kyauta, kada in ƙurashe halaliyata a game da bishara.

19. Ko da yake ni ba bawan kowa ba ne, na mai da kaina bawan kowa, domin in rinjayi mutane masu yawa.

20. Ga Yahudawa, sai na zama kamar Bayahude, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda Shari'a take iko da su, sai na zama kamar wanda Shari'a take iko da shi, ko da yake ba Shari'a take iko da ni ba, domin in rinjayi waɗanda Shari'a take iko da su ne.

21. Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne.

22. Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu.

Karanta cikakken babi 1 Kor 9