Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 5:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Fāriyarku ba shi da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa?

7. Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu.

8. Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.

9. Na rubuta muku a cikin wasiƙata, cewa kada ku yi cuɗanya da fasikai.

10. Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita, da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya.

11. Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.

12. Ina ruwana da hukunta waɗanda ba namu ba? Ba waɗanda suke a cikin Ikkilisiya za ku hukunta ba?

13. Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.

Karanta cikakken babi 1 Kor 5