Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 1:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. wanda zai tabbatar da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

9. Allah mai alkawari ne, shi ne kuma ya kira ku ga tarayya da Ɗansa Yesu Almasihu Ubangijinmu.

10. Na roƙe ku 'yan'uwa, saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, cewa dukanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga a tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna da nufi ɗaya, ra'ayinku ɗaya.

11. Don kuwa, ya 'yan'uwana, mutanen gidan Kuluwi sun ba ni labari, cewa akwai jayayya a tsakaninku.

12. Abin da nake nufi, shi ne kowannenku yana faɗar abu dabam, “Ni na Bulus ne,” wani kuwa, “Ni na Afolos ne,” wani kuwa, “Ni na Kefas ne,” ko kuwa, “ni na Almasihu ne.”

13. Ashe, Almasihu a rarrabe yake? Ko Bulus ne aka gicciye dominku? Ko kuwa an yi muku baftisma ne da sunan Bulus?

14. Na gode Allah da ban yi wa waninku baftisma ba, banda Kirisbus da Gayus,

15. kada wani ya ce da sunana ne aka yi muku baftisma.

16. Ai, kuwa lalle na yi wa jama'ar gidan Istifanas ma. Amma banda waɗannan ban san ko na yi wa wani baftisma ba.

17. Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.

Karanta cikakken babi 1 Kor 1