Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 9:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ubangiji kuma yana gāba da Hamat wadda yake kan iyaka, yana kuma gāba da Taya da Sidon ko da yake suna da hikima ƙwarai.

3. Taya ta gina wa kanta kagara,Ta kuma tara azurfa kamar ƙura,Zinariya kuma kamar sharar titi.

4. Amma Ubangiji zai washe ta,Ya zubar da dukiyarta a cikin teku,Wuta kuma za ta cinye ta.

5. Ubangiji ya ce,“Ashkelon za ta gani ta ji tsoro,Gaza kuma za ta yi makyarkyata da azaba,Haka kuma Ekron za ta fid da zuciya,Sarki zai halaka cikin Gaza,Ashkelon za ta zama kufai.

6. Tattarmuka za su zauna a Ashdod,Zan kuma sa alfarmar Filistiya ta ƙare.

7. Zan kawar da jininsu daga bakinsu,Da kuma haramtattun abubuwa daga haƙoransu.Sauransu za su zama jama'ar Allahnmu,Za su zama kamar sarki cikin Yahuza.Mutanen Ekron za su zama kamar Yebusiyawa.

Karanta cikakken babi Zak 9