Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 8:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji Mai Runduna kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ni Ubangiji Mai Runduna ina kishin Sihiyona ƙwarai.

3. Zan koma wurin Sihiyona, in zauna a tsakiyar Urushalima. Za a ce da Urushalima birnin gaskiya, da kuma dutsen Ubangiji Mai Runduna, tsattsarkan dutse.

4. Tsofaffi, mata, da maza, za su zauna a titunan Urushalima, kowa yana tokare da sanda saboda tsufa.

5. Samari da 'yan mata zan sa su cika titunan Urushalima, suna wasa.

6. “Idan abin nan ya zama mawuyaci ga sauran jama'a a kwanakin nan, zai zama mawuyacin abu ne a gare ni?

7. Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, zan ceci mutanena daga ƙasar gabas da ƙasar yamma.

8. Zan kawo su su zauna a Urushalima. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu da gaskiya da adalci.

9. “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.

10. Gama kafin waɗannan kwanaki, mutum da dabba ba su da abin yi. Ba kuma zaman lafiya ga mai fita da shiga saboda maƙiya, gama na sa kowane mutum ya ƙi ɗan'uwansa.

11. Amma yanzu ba zan yi da sauran jama'an nan kamar yadda na yi a kwanakin dā ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

12. Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama'an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.

Karanta cikakken babi Zak 8