Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 7:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. in faɗa wa dukan mutanen ƙasar da firistoci, in ce, “Sa'ad da kuka yi azumi da baƙin ciki a watan biyar da na bakwai dukan shekarun nan saba'in, saboda ni ne kuka yi azumin?

6. Sa'ad da kuma kuke ci, kuna sha, ba don kanku ne kuke ci, kuke sha ba?”

7. Maganar ke nan da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabawan dā, a lokacin akwai mutane da arziki cikin Urushalima da garuruwa kewaye da ita, a lokacin kuma akwai mutane a Negeb da gindin tuddai.

8. Ubangiji kuma ya yi magana da Zakariya, ya ce,

9. “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce ku yi shari'ar gaskiya, bari kowa ya nuna alheri da jinƙai ga ɗan'uwansa.

10. Kada kuma ku zalunci gwauruwa, wato wadda mijinta ya rasu, da maraya, da baƙo, da matalauci, kada kuma waninku ya shirya wa ɗan'uwansa mugunta a zuciyarsa.

11. “Amma suka ƙi ji, suka ba da baya, suka toshe kunnuwansu don kada su ji.

12. Suka taurare zuciyarsu kamar dutse don kada su ji dokoki da maganar da ni Ubangiji Mai Runduna na aiko ta wurin Ruhuna zuwa ga annabawa na dā. Domin haka ni Ubangiji Mai Runduna na aukar musu da hasala mai zafi.

13. Kamar yadda na yi kira suka ƙi ji, haka kuma suka yi kira, ni ma na ƙi ji.

14. Na sa guguwa ta warwatsa su a cikin al'ummai da ba su san su ba. Ƙasar da suka bari ta zama kango, ba mai kai da kawowa a cikinta. Ƙasa mai kyau ta zama kango.”

Karanta cikakken babi Zak 7