Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 3:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai ni kuma na ce, “Bari kuma su naɗa masa rawani mai tsabta.” Suka kuwa naɗa masa rawani mai tsabta, suka kuma sa masa riguna sa'ad da mala'ikan Ubangiji yana nan a tsaye.

6. Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya gargaɗi Yoshuwa, ya ce,

7. “Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Idan ka yi tafiya a hanyata, ka kuma kiyaye umarnina, zan sa ka zama shugaban Haikalina, ka lura da shirayina, zan kuma sa ka sami damar zuwa wurin waɗannan da yake tsaye.

8. Ka ji, ya Yoshuwa, babban firist, kai da abokanka da suke zaune gabanka, ku alama ce mai kyau. Ga shi, zan kawo bawana mai suna Reshe.

9. Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a kan dutsen da na kafa a gaban Yoshuwa, dutse mai ido bakwai zan yi rubutu, zan kawar da laifin al'umman nan rana ɗaya.

10. A wannan rana kowane ɗayanku zai gayyaci maƙwabcinsa zuwa gindin kurangar inabinsa da itacen ɓaurensa.’ ”

Karanta cikakken babi Zak 3