Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 3:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsauta maka, kai Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima ya tsauta maka. Ai, wannan mutum kamar itace ne wanda aka fizge daga cikin wuta.”

3. Yoshuwa dai yana tsaye a gaban mala'ikan saye da riguna masu dauɗa.

4. Mala'ikan kuwa ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku tuɓe masa rigunan nan masu dauɗa.” Sa'an nan ya ce wa Yoshuwa, “Ga shi, na kawar maka da laifinka, zan sa maka riguna masu daraja.”

5. Sai ni kuma na ce, “Bari kuma su naɗa masa rawani mai tsabta.” Suka kuwa naɗa masa rawani mai tsabta, suka kuma sa masa riguna sa'ad da mala'ikan Ubangiji yana nan a tsaye.

Karanta cikakken babi Zak 3