Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 14:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.

3. Sa'an nan Ubangiji zai tafi ya yi yaƙi da waɗannan al'ummai kamar yadda ya yi a dā.

4. A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.

5. Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa'an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa!

6. A wannan rana ba haske. Masu ba da haske za su dushe.

7. Ubangiji ne ya san wannan rana. Ba rana ba dare. Da maraice ma akwai haske.

8. A wannan rana ruwa mai rai zai gudano daga Urushalima. Rabinsa zai nufi tekun Gishiri, rabi kuma zai nufi Bahar Rum. Zai riƙa malalowa rani da damuna.

Karanta cikakken babi Zak 14