Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 14:17-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Idan kuwa wata al'umma a duniya ba ta haura zuwa Urushalima domin ta yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarki sujada ba, ba za a yi mata ruwan sama ba.

18. Idan al'ummar Masar ba ta halarci Idin Bukkoki ba, ba za a yi mata ruwan sama ba. Ubangiji kuma zai kawo mata irin annobar da ya kawo wa al'umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

19. Wannan shi ne hukuncin da za a yi wa Masar da dukan al'umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

20. A wannan rana za a zāna waɗannan kalmomi, wato “Mai Tsarki ga Ubangiji” a kan ƙararrawar dawakai. Tukwanen da suke Haikalin Ubangiji za su zama kamar kwanonin da suke a gaban bagade.

21. Kowace tukunya da take a Urushalima da Yahuza za ta zama tsattsarka ga Ubangiji Mai Runduna domin dukan masu miƙa hadaya su ɗauka su dafa naman hadaya a cikinsu. A wannan rana ba za a ƙara samun mai ciniki a Haikalin Ubangiji Mai Runduna ba.

Karanta cikakken babi Zak 14