Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 12:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga maganar Ubangiji game da Isra'ila. Ubangiji wanda ya shimfiɗa sammai, ya kirkiro duniya, ya kuma sa rai a cikin mutum, ya ce,

2. “Ga shi, ina gab da sa Urushalima ta zama ƙoƙon sa tangaɗi ga dukan al'ummai da yake kewaye. Yaƙin da zai kewaye Urushalima zai shafi Yahuza ita ma.

3. A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al'ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al'umman duniya za su taru su kewaye ta.

4. A wannan rana zan firgita kowane doki, in sa mahayinsa ya haukace. Zan lura da mutanen Yahuza, amma zan makantar da dawakan abokan gābansu.

5. Sa'an nan iyalan Yahuza za su ce wa kansu, ‘Ubangiji Allah Maɗaukaki yana ƙarfafa mutanensa waɗanda suke zaune a Urushalima.’

Karanta cikakken babi Zak 12