Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 11:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ki buɗe ƙofofinki, ke Lebanon,Don wuta ta cinye itatuwan al'ul naki.

2. Ka yi kuka, kai itacen kasharina,Gama itacen al'ul ya riga ya fāɗi,Itatuwa masu daraja sun lalace,Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan,Saboda an sassare itatuwan babban kurmi.

3. Ku ji kukan makiyaya,Gama an ɓata musu darajarsu.Ji rurin zakoki,Gama an lalatar da jejin Urdun.

4. Ga abin da Ubangiji Allah ya faɗa, “Ka zama makiyayin garken tumakin da za a yanka.

5. Masu sayensu za su yanyanka su, ba za a kuwa hukunta su ba. Masu sayar da su kuma za su yi hamdala gare ni, su ce sun sami dukiya. Makiyayansu kuwa ba su ji tausayinsu ba.

6. “Gama ba zan ƙara jin tausayin mazaunan ƙasan nan ba, ni Ubangiji na faɗa. Ga shi, zan sa su fāɗa a hannun junansu da a hannun sarkinsu. Za su lalatar da ƙasar, ba kuwa zan cece su daga hannunsu ba.”

7. Sai na zama makiyayi na masu tumakin kore. Na kuwa ɗauko sanda biyu, na ce da ɗaya “Alheri,” ɗaya kuma na ce da shi “Haɗa Kai.” Sai na yi kiwon tumakin.

8. A wata guda na hallaka makiyayan nan uku, gama ban jure da su ba, su ma sun gaji da ni.

9. Sai na ce wa tumakin, ba zan yi kiwonsu ba, “Waɗanda za su mutu sai su mutu, waɗanda kuma za su hallaka, to, sai su hallaka. Sauran da suka ragu kuma, su yi ta cin naman junansu!”

10. Sa'an nan na ɗauki sandana, wato “Alheri,” na karya shi, alama ke nan da ta nuna na keta alkawarin da na yi wa al'ummai duka.

11. Da haka aka karya alkawarina a wannan rana. Masu tumakin kore suna tsaye suna kallon abin da na yi, sai suka gane lalle wannan maganar Ubangiji ce.

Karanta cikakken babi Zak 11