Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 1:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”

7. A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato watan Shebat, a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya kuma yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo.

8. Da dare, na ga mutum yana kan aharashin doki, yana tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙi, a kwari. A bayansa kuma ga wani aharashin doki, da bidi, da kili.

9. Sai na ce, “Mene ne waɗannan, ya Ubangiji?”Mala'ikan da ya yi magana da ni ya ce, “Zan bayyana maka ma'anarsu.”

10. Sai mutumin da yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin ya amsa ya ce, “Waɗannan su ne Ubangiji ya aike su su yi tsaron duniya, suna kai da kawowa.”

11. Sai suka ce wa mala'ikan Ubangiji wanda yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun yi ta kai da kawowa a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”

12. Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, har yaushe za ka ƙi nuna jinƙai ga Urushalima da biranen Yahuza, waɗanda kake jin haushinsu shekara saba'in ke nan?”

13. Sai Ubangiji ya amsa wa mala'ikan da yake magana da ni da magana ta alheri da ta ta'azantarwa.

14. Mala'ikan kuma da yake magana da ni ya ce, in yi shela in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce yana jin ƙishin Urushalima da Sihiyona ƙwarai.

15. Yana fushi ƙwarai da al'umman duniya da take zaman lafiya, gama ya yi ɗan fushi da mutanena, amma su suka yi musu hukuncin da ya zarce.

16. Saboda haka shi Ubangiji zai koma ya ji juyayin Urushalima. Za a gina Haikalinsa a cikinta, zai kuma auna Urushalima da ma'auni.”

Karanta cikakken babi Zak 1