Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 9:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji,Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.

11. Ku yabi Ubangiji, shi da yake mulki a Sihiyona!Ku faɗa wa kowace al'umma abin da ya yi!

12. Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya,Ba ya mantawa da kukansu,Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu.

13. Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini!Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji,

14. Domin in iya tsayawa a gaban jama'ar Urushalima,In faɗa musu dukan abin da ya sa nake yabonka.Zan yi farin ciki saboda ka cece ni.

15. Arna sun haƙa rami sun kuwa fāɗa ciki,Sun ɗana tarko, ya kuwa kama su.

16. Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci,Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.

17. Mutuwa ce maƙarar dukan mugaye,Da dukan waɗanda suke ƙin Allah.

18. Ba kullum ne ake ƙyale masu bukata ba,Ba za a danne sa zuciyar waɗanda ake zalunta ba har abada.

19. Ka zo, ya Ubangiji! Kada ka bari mutane su gagare ka!Ka kawo arna a gabanka, ka hukunta su.

Karanta cikakken babi Zab 9