Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 7:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ka tsai da muguntar mugaye,Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki.Kai Allah mai adalci ne,Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.

10. Allah ne mai kiyaye ni,Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya.

11. Allah alƙali ne mai adalci,Kullum kuwa yana kā da mugaye.

12. Idan mutane ba su tuba ba,Allah zai wasa takobinsa,

13. Zai ɗana bakansa ya shirya shi,Zai ɗauki makamansa masu dafi,Ya kuma auna kibansa masu wuta.

14. Ka duba, yadda mugu yake tunanin mugunta a ransa,Yana shisshirya wahala, yana kuma aikata ruɗi.

15. Yana haƙa rami mai zurfi a ƙasa,Sa'an nan yă fāɗa ramin da ya haƙa!

16. Saboda haka muguntarsa ta hukunta shi ke nan,Rikicin kansa ya yi masa lahani.

17. Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa,Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki.

Karanta cikakken babi Zab 7