Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 7:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, Allahna, na sami mafaka a wurinka,Ka cece ni, ka tserar da ni daga dukan masu fafarata,

2. Idan ba haka ba kuwa, za su ɗauke ni,Su tafi da ni zuwa wurin da ba wanda zai cece ni,A can za su yayyage ni kamar zaki.

3. Ya Ubangiji, Allahna, idan na aikata ɗaya daga cikin waɗannan,Wato idan na yi wa wani laifi,

4. Idan na ci amanar abokina,Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili,

5. To, bari abokan gābana su fafare ni, su kama ni,Bari su datse ni har ƙasa, su kuma kashe ni,Su bar ni ƙasa, matacce!

Karanta cikakken babi Zab 7