Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 68:19-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ku yabi Ubangiji,Wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum,Shi ne Allah wanda ya cece mu.

20. Allahnmu, Allah Mai Ceto ne,Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu,Wanda yake cetonmu daga mutuwa.

21. Hakika Allah zai farfashe kawunan abokan gābansa,Da na waɗanda suka nace bin hanyoyinsu na zunubi.

22. Ubangiji ya ce, “Zan komo da su daga Bashan,Zan komo da su daga zurfin teku,

23. Don ku wanke sawayenku a cikin jinin maƙiyanku,Karnukanku kuwa za su lashe iyakar abin da suke so.”

24. Ya Allah, jama'a duka sun ga irin tafiyarka ta nasara,Irin tafiyar Allah, Sarkina, zuwa tsattsarkan wurinsa.

25. Mawaƙa suna kan gaba, mabusa suna biye,A tsakiya kuwa 'yan mata suna kaɗa bandiri.

26. “Ku jama'ar Allah, ku yabe shi cikin taronku,Ku yabi Ubangiji, dukanku, ku zuriyar Isra'ila!”

27. Ga Biliyaminu mafi ƙanƙantaCikin kabilai, a kan gaba,Sa'an nan shugabannin Yahuza da ƙungiyarsu,Daga nan sai shugabannin Zabaluna da na Naftali suna biye da su.

28. Ka nuna ikonka, ya Allah,Ikon nan da ka nuna saboda mu.

29. Daga Haikalinka a Urushalima,Sarakuna sukan kawo maka kyautai.

30. Ka tsauta wa Masar, naman jejin nanMai zafin hali da yake cikin iwa,Ka tsauta wa sauran al'umma, taron bijiman nan da 'yan maruƙansu,Har dukansu su durƙusa, su miƙa maka azurfarsu.Ka warwatsar da jama'ar nanMasu son yin yaƙi!

Karanta cikakken babi Zab 68