Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 66:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yabi Allah da babbar murya ta farin ciki,Ya jama'a duka!

2. Ku raira waƙar darajar sunansa,Ku yabe shi da ɗaukaka!

3. Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawaSuna da banmamaki ƙwarai!Ikonka yana da girma ƙwarai,Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.

4. Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada,Yana raira maka waƙar yabbai,Yana raira yabbai ga sunanka.”

5. Zo, ka ga abin da Allah ya yi,Ayyukansa masu ban al'ajabiWaɗanda ya aikata ga mutane.

6. Ya sa teku ta zama busasshiyar ƙasa,Kakanninmu suka haye kogi da ƙafa.A can muka yi farin ciki saboda abin da ya yi.

7. Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa,Yana duban al'ummai,Don kada 'yan tawaye su tayar masa!

8. Ku yabi Allahnmu, ya ku dukan al'ummai,Bari a ji yabon da kuke yi masa.

9. Shi ne yake rayar da mu,Bai kuwa yarda mu fāɗi ba.

10. Ka jarraba mu, ya Allah,Kamar yadda ake tace azurfa da wuta,Haka nan ka jarraba mu.

Karanta cikakken babi Zab 66