Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 65:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Allah, dole mutane su yabe ka a Sihiyona,Tilas su ba ka abin da suka alkawarta.

2. Saboda kakan amsa addu'o'i,Dukan mutane za su zo wurinka.

3. Zunubanmu sun kāshe mu,Amma za ka gafarta zunubanmu.

4. Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe suSu zauna a tsattsarkan wurinka!Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka,Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!

5. Ka amsa mana, ya Allah Mai Cetonmu,Ka kuma cece mu ta wurin aikata al'amuran banmamaki.Mutane daga ko'ina a duniya,Har da waɗanda suke can nesa a hayin tekuna,Sun dogara gare ka.

6. Ka kakkafa duwatsu ta wurin ikonka,Ka bayyana ƙarfin ikonka.

7. Kakan kwantar da rurin tekuna,Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa,Kakan kwantar da tarzomar jama'a.

8. Dukan duniya ta tsorata,Saboda manyan ayyuka da ka aikata.Ayyukanka sukan kawo sowa ta farin cikiDaga wannan iyakar duniya zuwa wancan.

9. Kakan nuna kana kulawa da ƙasar,Ta wurin aiko mata da ruwa.Ka arzuta ta, ta zama dausayi.Rafuffukan da ka bayar ba su taɓa ƙafewa ba,Sun sa ƙasar ta ba da amfanin gonaki,Abubuwan da ka aikata ke nan.

Karanta cikakken babi Zab 65