Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 62:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga Allah kaɗai na dogara,Cetona daga gare shi yake fitowa.

2. Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,Shi ne kariyata,Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.

3. Har yaushe dukanku za ku fāɗa wa wani don ku yi nasara da shi,Kamar rusasshen garu,Ko kuma dangar da ta fāɗi?

4. Ba abin da kuke so, sai ku ƙasƙantar da shi daga maƙaminsa na daraja,Kuna jin daɗin yin ƙarairayi.Kuna sa masa albarka,Amma a zuciyarku la'antarwa kuke yi.

5. Ga Allah kaɗai na dogara,A gare shi na sa zuciyata.

6. Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,Shi ne kariyata,Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.

7. Cetona da darajata daga Allah ne,Shi ne ƙaƙƙarfan makiyayina,Shi ne mafakata.

Karanta cikakken babi Zab 62