Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 50:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Da ina jin yunwa ba sai na faɗa muku ba,Gama da duniya da dukan abin da yake cikinta nawa ne.

13. Nakan ci naman bijimai ne?Ko nakan sha jinin awaki?

14. Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya,Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.

15. Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo,Zan cece ku,Ku kuwa za ku yabe ni.”

16. Amma Allah ya ce wa mugaye,“Don me za ku haddace umarnaina?Don me za ku yi magana a kan alkawaraina?

17. Kun ƙi in tsauta muku,Kun yi watsi da umarnaina.

18. Sa'ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi.Kuna haɗa kai da mazinata.

19. “Kullum a shirye kuke ku hurta mugunta,Ba ku jin nauyin faɗar ƙarya.

20. A shirye kuke ku sari 'yan'uwanku,Ku sa musu laifi.

21. Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba,Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake.Amma yanzu zan tsauta muku,In bayyana muku al'amarin a fili.

Karanta cikakken babi Zab 50