Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 38:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Saboda wawancina, miyakuna sun ruɓe, suna wari,

6. An tanƙware ni, an ragargaza ni,Ina ta kuka dukan yini.

7. Ina fama da zazzaɓi,Ina rashin lafiya ƙwarai.

8. An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina,Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.

9. Ka san bukatata, ya Ubangiji,Kana jin dukan nishe-nishena.

10. Zuciyata tana ɗar, ƙarfina ya ƙāre,Idanuna sun dushe.

11. Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna,Har iyalina ma sun guje mini.

12. Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna,Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni,Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.

13. Kamar kurma nake, ba na iya ji,Kamar kuma bebe, ba na iya magana.

14. Ni kamar mutumin da ba ya iya amsawa nake, don ba na ji.

15. Na dogara gare ka, ya Ubangiji,Kai za ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.

16. Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata.Kada ka bar su su yi kirari a kan faɗuwata!

17. Ina gab da fāɗuwa,Ina cikin azaba kullum.

Karanta cikakken babi Zab 38