Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 38:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kada ka yi fushi har ka tsauta mini, ya Ubangiji!Kada ka hukunta ni da fushinka!

2. Ka hukunta ni, ka kuwa yi mini rauni,Ka kuma buge ni har ƙasa.

3. Saboda fushinka ina ciwo mai tsanani,Duk jikina ya kamu da ciwo saboda zunubina.

4. Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina,Ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.

5. Saboda wawancina, miyakuna sun ruɓe, suna wari,

6. An tanƙware ni, an ragargaza ni,Ina ta kuka dukan yini.

7. Ina fama da zazzaɓi,Ina rashin lafiya ƙwarai.

8. An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina,Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.

9. Ka san bukatata, ya Ubangiji,Kana jin dukan nishe-nishena.

10. Zuciyata tana ɗar, ƙarfina ya ƙāre,Idanuna sun dushe.

11. Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna,Har iyalina ma sun guje mini.

12. Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna,Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni,Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.

Karanta cikakken babi Zab 38