Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 17:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ba su jin tausayi, suna magana da girmankai,

11. Yanzu suna kewaye da ni duk inda na juya,Suna jira su sami dama su fyaɗa ni ƙasa.

12. Kamar zakoki suke nema su yayyage ni kaca-kaca,Kamar sagarun zakoki suna fakona a wurin ɓuyarsu.

13. Ka zo, ya Ubangiji,Ka yi yaƙi da maƙiyana, ka yi nasara da su!Ka cece ni da takobinka daga mugaye,

14. Ka cece ni daga gare su da ikonka,Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyan nan,Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu,Ka sa har 'ya'yansu, su ma, ta ishe su,Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!

15. Zan gan ka domin ni adali ne,Sa'ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.

Karanta cikakken babi Zab 17