Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 1:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. A wannan rana zan karya bakan Isra'ila a kwarin Yezreyel.”

6. Gomer ta kuma ɗauki ciki, ta haifi 'ya mace. Ubangiji kuma ya ce wa Yusha'u, “Ka raɗa mata suna Bajinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama'ar Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata.

7. Amma zan yi wa mutanen Yahuza jinƙai. Ni kaina zan cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ka da dawakai, ko da sojojin dawakai ba.”

8. Sa'ad da ta yaye Ba-jinƙai, ta sāke ɗaukar ciki, ta haifi ɗa namiji.

9. Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne,ni kuma ba Allahnku ba ne.

10. “Duk da haka yawan mutanen Isra'ilaZai zama kamar yashi a bakin teku,Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba.Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’

11. Mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila za su haɗu su zama ɗaya,Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya.Za su shugabanci ƙasarGama ranar Yezreyel babba ce.”

Karanta cikakken babi Yush 1