Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 3:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka tsai da shawara, cewa kowa da kowa ya yi azumi. Dukan mutane kuwa babba da yaro, suka sa tufafin makoki.

6. Sa'ad da Sarkin Nineba ya ji labarin, sai ya sauka daga kursiyinsa, ya tuɓe rigarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.

7. Sai ya aika wa mutanen Nineba da sanarwa cewa, “Wannan doka ce daga sarki da majalisarsa. Kada kowa ya ci wani abu, mutane, da shanu, da tumaki, da awaki duka, kada kowa ya ci, ko ya sha ruwa.

8. Sai dukan mutane da dabbobi su sa tufafin makoki. Kowa ya roƙi Allah da gaske, kowa kuma ya bar mugayen ayyukan da yake yi.

9. Kila Allah zai dakatar da nufinsa, fushinsa ya huce, ya bar mu mu tsira daga mutuwa!”

Karanta cikakken babi Yun 3