Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 1:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Amma maimakon Yunusa yă tafi, sai ya gudu daga wurin Ubangiji zuwa Tarshish. Ya tafi Yafa, nan ya sami jirgin ruwa yana gab da tashi zuwa Tarshish, ya kuwa biya kuɗinsa, ya shiga tare da masu jirgin zuwa can don yă tsere wa Ubangiji.

4. Amma Ubangiji ya aika da iska mai ƙarfi a tekun, hadirin ya tsananta ƙwarai har jirgin yana bakin farfashewa.

5. Dukan matuƙan jirgin suka firgita, sai kowannensu ya shiga roƙon allahnsa. Suka yi ta jefar da kayan da suke cikin jirgin a ruwa don su sami sauƙi. Yunusa kuwa yana can cikin jirgi, a kwance, yana ta sharar barci.

6. Can shugaban jirgin ya iske shi, ya ce masa, “Me ya sa kake barci? Tashi ka roƙi allahnka, watakila allahnka zai ji tausayinmu, yă cece mu.”

7. Matuƙan jirgin kuwa suka ce wa junansu, “To, bari mu jefa kuri'a mu gani ko alhakin wane ne ya jawo mana wannan bala'i da muke ciki.” Sai suka jefa kuri'a, kuri'ar kuwa ta fāɗa a kan Yunusa.

8. Suka ce masa, “Ka faɗa mana, laifin wane ne ya jawo mana wannan masifa? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Daga wace al'umma kake?”

Karanta cikakken babi Yun 1