Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 5:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata,Ina tattara mur da ƙaro.Ina shan zuma da kakinsa.Ina shan ruwan inabi da madara kuma.Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!

2. Ina barci, amma zuciyata na a farke,Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa.Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata,Wadda ba wanda zai kushe ki.Kaina ya jiƙe da raɓa,Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.

3. Na riga na tuɓe tufafina, in sāke sa su kuma?Na wanke ƙafafuna, in sāke ɓata su?

4. Ƙaunataccena ya janye hannunsa daga ƙofa,Zuciyata kuwa tana kansa.

5. Sai na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, ya shigo.Hannuna sharkaf da mur,Yatsuna suna ɗiga da mur sa'ad da na kama hannun ƙofar.

6. Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ya riga ya tafi!Na so in ji muryarsa ƙwarai!Na neme shi, amma ban same shi ba.Na yi kiransa, amma ba amsa.

Karanta cikakken babi W. W. 5